ABNA24 : Wadanda su ka rasa rayukan nasu su ne;Jakadan na Italiya Luca Attanasio dan shekaru 43, da jami’in tsaro Vittorio Lcovacci, mai shekaru 30, sai kuma matukun motar hukumar abinci ta duniya da ba a ambata sunansa ba.
Maharan da su ka bude wuta sun ji wa jakadan raununa da kuma sauran mutanen da suke tare da shi, sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar fitar da shi zuwa asibitin garin Goma.
Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin a yankin da yake kunshe da kungiyoyi masu dauke da makamai.
342/